ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar ta Faransa ya bayyana cewa a ‘yan sa’o’in da ya yi a kasar Iraqi, shugaban kasar na Faransa ya gana da shuwagabannin kasar, wadanda suka hada da shugaban kasa Barham Saleh da kuma Firai minista Mustaga Alkazimi.
Bangarorin biyu sun tattauna batutuwa da dama daga cikin har da na tsaro da kuma da kuma makamashi.
Macron ya bukaci gwamnatin kasar Iraqi ta zama mai cikken ‘yanci a dai-dai lokacin da kasashen Iran da Amurka suke rigima dangane da al-amura a kasar ta Iraqi.
Shugaba Barham Saleh ya ce yana dakon ganin ziyarar Macron zuwa kasar Iraqi a cikin shekara ta 2021 mai kamawa.
A yayinda Firai ministan kasar ta Iraqi ya bukaci Faransa da kuma dukkan kasashen turai su taimaka don ganin kasar Iraqi ta samu zaman lafiya mai dorewa a kasar.
Kasar Faransa dai tana daga cikin kasashen kawance masu yaki da Daesh a kasar Iraqi karkashin jagorancin Amurka.
342/